Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Talata ta ce an kashe ‘yan bindiga 50 a yankin Birnin Gwari, ta hanyar hadin gwiwar rundunar soji Nigeria.
Mista Samuel Aruwan Kwamishina, Ma’aikatar Tsaro da kula da harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna ya tabbatar da haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Inda Sanarwar ta ce, “Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga sama da 50 a yayin kai hare-hare ta kasa da ta sama a yankin Saulawa da Farin Ruwa na Karamar Hukumar Birnin Gwari.”
Sanarwar ta kuma ce, Gwamnatin Jihar Kaduna tare da Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwar, sun bada Umarni ga wani jirgi mai saukar ungulu na Sojojin Sama na Nigeria, da ya taimaka wa sojojin kasa da ke aiki a dogon Dawa, Damari zuwa Saulawa wurin Kai harin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun Budewa Sarakunan Gargajiya Wuta a taro a Imo
Ya ce sakamakon binciken da ake yi, an hangi ‘yan bindiga a kan babura biyar, kusan kilomita 4 gabas da Saulawa, suna so suyi wa soji kwanton bauna, inda jirgin helikwafta ya Maida musu da martani ta sama.
“Bayan wannan, an ga‘ yan bindiga dauke da babura kusan 50 sun arce zuwa Farin Ruwa, kuma jirgin Saman ya farmake, yayin da Sojojin kasa suka tarwatsa ragowar wadanda suka tsere, ”in ji shi
Ya kara da cewa jirgin helikwafta na biyu ya taimaka wajan samamen, kuma an kashe wasu da yawa daga cikin ‘yan bindigar da suka tsere ta hanyar kai hare -hare, ya kara da cewa, an kashe’ yan ta’adda sama da 50 yayin aikin hadin gwiwar.
Gwamna Nasir El-Rufa’i ya nuna gamsuwarsa game da aikin jami’an sojin, kuma ya taya sojoji murnar samun nasarar.
Kazalika ya bukace su da su ci gaba da kawo karshen hare -haren da ‘yan bindiga ke kai wa a fadin jihar Kaduna.
Comments 1