Rundunar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da ‘yan banga sun ceto akalla mutane goma sha biyar da wasu ‘yan bindiga suka sace a kauyen Jellako da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Rundunar ‘yan sandan jihar wacce ta bayyana hakan ta bakin jami’in hulda da jama’a na jihar, DSP Wasiu Abiodun a garin Minna, ya ce rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaron ta kama ‘yan bindigar ne a yankin, har ta kai ga kwato mutane 15 da aka yi garkuwa da su.
Ya bayyana cewa, a sakamakon musayan wuta da jami’an tsaron suka yi da ‘yan ta’addan wasu daga cikinsu sun tsere zuwa cikin dajin da raunukan harbin bindiga, Kuma an kwato babura biyu a yayin artabun.
A cewarsa, “hakan wani bangare ne na kokarin dakile ko kuma kawar da ‘yan fashi da sauran masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar,
Ya ce “Lamarin ya gudana ne a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2022, bisa ga bayanan da aka samu cewa an ga wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami ne. A kauyen Jellako, na karamar hukumar Rafi, rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro tare da ‘yan banga, sun yi artabu da su a yankin ”.
“Yayin da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su domin tsira da rayukansu, sun yi watsi da babura biyu da wasu mutane goma sha biyar da aka sace a wurare daban-daban a jihar.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya bayyana cewa, tawagar sun ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba, sannan aka kai su wani asibiti da ke kusa domin kula da lafiyarsu.
“Daga baya wadanda abin ya shafa za a haduwa da iyalansu” in ji shi.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma kara tabbatar wa da jama’a cewa rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yakar ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka har sai an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da ‘yan fashin suka mamaye.
Comments 1