Wasu daga cikin Mayakan ISWAP wadanda ba a san adadin su ba sun mutu , bayan arangamar da suka yi da jami’an tsaron hadin guiwa, a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu na jihar Borno.
Mayakan kungiyar, wadanda aka gani cikin kayan soji, sun kai farmaki ga wata tawagar jami’an ‘yan sanda, a yammacin Juma’ar da ta gabata, ya yin da suke dawo wa daga yankin Buni Yadi, na kusa da Auno-Garin Kuturu, a karamar hukumar Kaga dake jihar.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan, sun kwace wata mota daya, mallakin jami’an tsaron.
Sai dai daga bisani martanin gaggawa da dakarun sojin sama na runduna ta 212, bataliya ta 73, tare da runduna ta 134 da bataliya ta 199, suka kai, ya janyo ajalin ‘yan ta’addan da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta baje kolin wani dalibi a Zamfara
Wata majiya daga rundunar sojin kasar nan, ta ce, sojojin sun bayyana ta jiragen yaki, inda suka dinga mai da wa ‘yan ta’addan wuta, a kauyen Malam Fantari.
Kazalika wasu daga cikin Yan ta’addan sun sami mummunan raunika, inda suka bar ababen hawansu Kuma suka gudu, domin neman hanyar tsira da rayu kar su.