By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) ta gano haramtacciyar kasuwar kifi ta Boko Haram a lungu da sako na gabar tafkin Chadi tare da cafke mutane 30 da suka yi ikirarin cewa su masunta ne kuma manoma, kamar yadda majiyar soja ta bayyana.
An ce an gano kasuwar ne wanda ta kasance cibiyar samar da kudaden shiga ga ‘yan ta’adda da suke sayen makamai da alburusai da su.
“Dakarun sun gano kasuwar kifi ne a lokacin da suke sintiri na dogon zango a Tamfalla, sananniyar cibiyar kamun kifi da ke cikin yankin karamar hukumar Kukawa”, in ji daya daga cikin majiyoyin.
Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro da ke da masaniya a tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tabbatar da kama ‘yan ta’addan.
Da yake karin bayani kan wannan samame, babban jami’in yada labarai na rundunar soji, HQ MNJTF N’Djamena, Laftanar Kanal Kamarudeen Adegoke, ya ce an kama wasu matasa 30 da suka yi ikirarin cewa su masunta ne kuma manoma a yankin Doron Naira. kuma an bayyana su da kuma yi musu tambayoyi don a tabbatar da laifinsu ko akasin haka.
Ya ce abubuwan da aka samu a cikin yankin sun hada da kifaye a cikin kwali wadanda aka shirya su , da hatsi iri-iri, kayayyakin gidaje da kuma babur daya tilo.
An bayar da rahoton cewa ISWAP ta ci gaba da yakin ta’addanci ta hanyar kamun kifi, noma da kiwon shanu da sauran ayyukan zamantakewa da tattalin arziki a tafkin Chadi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta samu labarin cewa wasu ‘yan kasuwa daga Maiduguri, Adamawa, Monguno, Hadejia, Niger da Kamaru, sun kutsa cikin tafkin Chadi ta yankunan da a yanzu fararen hula ke yin zirga-zirga a yankin.
“A musaya, ISWAP na karbar harajin kudi naira 5,000 duk wata daga mutanen da suka bayyana suna son biya”, in ji wata majiya.
“Sun kuma tabbatar da hanyoyin kasuwanci, ma’ana cewa kayayyaki na yau da kullun – mafi mahimmancin su shine kiyaye ISWAP sosai – wanda zai iya isa tsibirin cikin sauƙi.