By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan RRS ta jihar Legas ta damke wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne ta Awawa Boys.
Hakan ya faru ne a wani samame da suka kai a cikin dare da rana a wuraren da ake kyautata zaton maboyar ‘yan kungiyar asiri ne a Mulero, Orile Agege, a yankin Abule Egba na jihar.
A ranar Laraba ne dai rundunar RRS ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne tare da mika su ga sashin ‘yan sanda na yankin.
A cikin wata sanarwa da RRS ta fitar, ta ce, “A amfani da bayanan sirrin da aka tattara sakamakon tada hankalin jama’a da aka yi a Mulero da wani bangare na Iyana Ipaja a daren ranar Talata, Kwamandan RRS, CSP Olayinka Egbeyemi, yana aiki da umarnin sabon kwamishinan ‘yan sanda, CP. Abiodun Alabi, ya tura ayarin motocin sintiri a dukkan al’ummar da abin ya shafa kafin su kai farmaki cikin dare a maboyar ‘yan ta’addan.
“Da safiyar yau za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda ya umarta.
“An samu wasu kayayyaki a wajen daya daga cikin wadanda ake zargin an nannade a wasu abubuwa da aka yi imanin cewa tabar wiwi ce da kankara.”