Rundunar sojojin Nijeriya sun fitar da jerin sunayen sojoji 22 da suke nema ruwa a jallo ciki kuwa harda mai mukamin Manjo wadanda ake zargin sun tsere a yayin da Boko Haram suka kai musu hari.
Ga jerin sunayen sojoji 22 da rundunar soja ta fitar wanda PREMIUM TIMES ta samu da ake nema ruwa a jallo, saboda ana zargin su da gudu a fagen daga da kuma taimakon Boko Haram.
Sojojin sune: Manjo U.A. Nagogo, Mallam Turaki, a staff sergeant; Benjamin Afolabi, sergeant, Christian Nwachukwu, sergeant; Patrick Kosin, sergeant; Awuwa Orin, sergeant; Ibrahim Amodu, sergeant; Nasiru Umar, sergeant; Bello Suleiman, sergeant; Josiah Seth, sergeant da Muazu Nura, sergeant.
Ayodeji Ogunsuji, corporal; Michael Friday, corporal; Wakili Saul, corporal; Akyen Zamani, corporal; Yahaya Abubakar-Doia, lance corporal; Isikuru Venture, lance corporal; Aminu Isiaku, lance corporal; Usman Suleiman, lance corporal; Maigari Markus, lance corporal; Edward Ofem, lance corporal da Adams Shehu, lance corporal.
Duk wanda ya gan su ya taimaka ya kai rahoto ofishin wata hukuma mafi kusa.