Hedikwatar rudunar tsaron soji ta Nijeriya ta ce daga ranar 18 ga watan Maris zuwa 5 ga watan Mayu sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram guda 343 a arewa maso gabashin Nijeriya a samame daban-daban da rundunar sojin ta kai.
Daraktan watsa labarai na Hedikwatar tsaron, Manjo Janar John Enenche, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a taron manema labarai a Abuja.
Har wala yau ya kara da cewa ‘yan ta’adda da dama suka raunata sakamakon musayar wuta da suka rika yi a tsakaninsu ciki wadanda suka kashe kuwa harda manyan Kwamandojin Boko Haram din a cewarsa.
Enenche ya ce sun kuma yi nasarar tarwatsa wuraren da Boko Haram ke shirya kai hare-hare daban-daban, sannan sun kama mutum 16 da suke yiwa Boko Haram din leken asiri.
Sannan ya ce a tsakanin jihohin Katsina da Zamfara a karkashin atisayen ‘Operation Hadarin Daji’ sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 146. Sannan sun ‘yanto mutum 17 da aka yi garkuwa da su. Kuma tuni ma suka hada su da iyalansu.
Sannan a cewarsa sun kuma ‘yanto shanu 922 da aka sace tare da Tumakai 446. Sai dai ya ce sojoji hudu sun rasa ransu sakamakon wannan gumurzun.