Hedikwatar tsaron Nijeriya ta musanta zargin da aka yi cewa sojoji ne suka kai hari ga ayarin motocin gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zullum.
A cewar sojin, ‘yan Boko Haram ne suka kai hari, ba kamar yadda ake cewa zagon kasa ne daga wajen jami’an tsaro.
Mako guda kenan cif da wasu masu dauke da makamai suka bude wuta kan ayarin gwamnan lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa garin Baga domin wata ziyarar aiki.