Bayan da ke shigowa Dimokuradiyya na nuni da cewa; hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce rundunar sojin kasar ta yi nasarar hallaka ‘yan bindiga uku tare da cafke hudu a wani samame da rundunar Whirl Stroke suka kai a ranar Asabar a jihar.
Shugaban sashen yada labarai na Hedikwatar tsaron, Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce sun kai samamen ne a kauyukan Tomatar Ugba da Kundi dake karamar hukumar Katsina-Ala na jihar.