Sojojin Najeriya sun gudanar da ayyukan bada Magunguna kiwon lafiya kyauta ga wasu al’ummomi a karamar hukumar Makurdi ta jihar Benue.
Kwamandan bataliya ta runduna ta 72, Lt-Col A. D. Alhassan ne ya jagoranci wannan aikin a sansanin ‘yan gudun hijira (IDPs) da ke Makurdi, a ranar Alhamis, ya ce wannan a wani yunkuri na ayyukan inganta zamantakewa tsakanin Al’uma da rundunar soji ta Nigeria.
“Sojojin Najeriya suna fara gudanar da wannan aikin ne, don kara inganta tsaro domin tabbatar da cewa, mazauna jihar sun more ragowar shekarar nan, a cikin yanayi na lumana,” in ji shi.
Ya bukaci mazauna yankin da su ba da gudummawar bayanai masu amfani ga sojojin, don dakile Matsalar rashin tsaro a Fadin jihar Baki daya.
KARANTA WANNAN. LABARIN: Babu wani shiri na dawo da SARS, inji IGP
Kwamandan ya yi bayanin cewa, bada agajin kayayyakin kiwon lafiya kyauta, ga al’umar yankunan, an yi shi don tallafawa kiwon lafiyar mutane.
A nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Makurdi, Anthony Dygeh, ya yabawa rundunar Sojojin Nigeria, kan wannan aiki da ta yi, tare da rokon jama’a da su shiga cikin aikin kula da kiwon lafiya.
Comments 1