A yau Alhamis, Shelkwatar tsaro ta kasa ta bayyana nasaran, kama wani da a ke zargin mamba ne a kungiyar ta da kayarbaya ta ISWAP, a yankin Sango Otta na jihar Ogun.
Mukaddashin Daraktan yada labarai na rundunar, Bernard Onyeuko ne a sanarwa wannan cigaban da aka samu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ta ce, rundunar tsaron kasar nan, ta kama wanda ake zargin ne, a wasu same da ta kai, tun daga ranar 18 ga watan Yuni, zuwa jiya Laraba 30 ga watan Yunin shekaran nan.
Onyeuko ya ce, Rundunar AWATSE ce ta kama wanda ake zargin mai suna Ibrahim Musa, a wani same da ta kai wasu yankuna dake cikin jihar Ogun.
Sanarwar ta kuma ce, daga cikin wuraran da rundunar ta kai samame a Yankin Kudu maso Yammacin kasar nan, akwai: Yankin Majidun, inda a nan ne, ta kama Ibrahim Musa, daya daga cikin Yan kungiyar tada kayar baya ta ISWAP, a Gini mai lamba 31, dake kan hanyar Abartura na garin Sango-Ota, a jihar Ogun.
Onyeuko ya cigaba da cewa, wani rahoton sirri ya nuna cewa, Musa na kan hanyar shi ne na zuwa jihar Legas, domin amsan wasu kayayyaki wa kungiyar ISWAP, dake kai hare-hare a jihar Borno.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar yan sanda ta haramta gangami a legas
A karshe ya ce, Shugaban rundunar tsaro na Kasa Lucky Irabor, ya sanya wasu tsaffin janar-janar na soji a cikin kula da harkokin tsaro a yankin Kudu maso Yamma, domin magance matsalolin tsaron da kasar nan ke fuskanta.
undunar soji ta kama wani da ake zargin dan kungiyar ISWAP ne