Rundunar tsaron hadin gwuiwa da ke aiki a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, ta sami nasaran hallaka Yan ta’addan 11 da kwato wasu mungwan makamai, da kuma wata tanka, makare da man Fetur, a wani samame da ta kai a jihar Borno
Mai magana da yawun rundunar soji ta kasa Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi inda ya ce, rundunar hadaka na bataliya 82 ne, da ke aiki a kan hanyar Ngoshe zuwa Ashigashiya da ke da kimanin nisan kilomita 12 da sansanin na su, su kayi batakashi da Yan ta’addan Boko Haram a yankin Daushe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da Dalibai a wata makaranta dake Maraban Rido a Kaduan
Rundunar ta ce, nan take ta kashe yan ta’addan biyar, kuma ta kwace Kunshin harsashin AK-47 daya, da wasu makamai da dama.
Rundunar ta kuma ce, ko a ranar daya ga watan nan da muke ciki, sai da bataliya ta 212 suka kaddamar da hare-hare ga yan ta’addan a kan hanyar Gadayi-Karato-Gubio, da kyauyen Magumeri Tungushe, da kuma wasu unguwani dake kusa da yankin Kerenoa.
Kazalika a cewar sanarwar ko a ranar 2 ga watan 2 Yulin nan da muke ciki, rundunar sojin sai da ta farmaki Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, a kan hanyar Auno Jakana.
A karshe sanarwar tace, dukkannin nasarorin da rundunar ta ke samu, tana samunshi ne, bisa tallafin sashin na daya da na biyu na rundunar sojin Sama, dake kara yiwa yan ta’addan lugudan wuta ta sama.
“During the encounter, six terrorists were neutralised, three AK47s and one rocket-propelled grenade were captured, while one gun truck was destroyed. Two other gun trucks abandoned by the terrorists were also recovered,” added the army.