A ranar Talata shugaban rundunar sojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya lika wa sabbin janarorin da aka yi wa karin girma zuwa Manjo Janar da Birgediya Janar.
Bayani ya nuna cewa, sabbin Janarorin sun hada da Manjo janar 1 da kuma masu mukaman Birgediya Janar 22 wadanda hukumar rundunar sojin Nijeriya ta aminnce da karin girman nasu.
Kusan masu mukamin Birgedia 34 da masu mukanin Birgediya Janar 47 suka samu karin girman zuwa mukami na gaba.
Da yake taya su murna bayan an lika musu sabbin mukaman nasu, Burutai ya bukaci su ci gaba da tsayuwa kyam wajen gabatar da ayyukansu da tsarin mulkin Nijeriya ya dora musu.
Ya ce, sabbin mukaman ya dofa su akan matakin gudanarwa a kan haka ya bukaci su jajirce wajen sauke nauyin da ya doru akan su a halin yanzu.
A nasa jawabin, AVM Mohammed Usman, ya bayyana wa sabbin janarorin da su karbi wannna karin girmar a mastayin wani kyauta daga Allah.
Ya kuma nemi su kara kaimi wajen sauke nauyin da tsarin mulkiin kasa ya dora musu kuma su kallai karin girmar a mastayin wani karin nauyi na aiki.
Haka kuma Laftanar Janar Lamidi Adeosun, ya bukaci sabbin janarorin su kara kaimi wajen ganin sun rungumi dukkan abokan aikinsu ba tare da nuna bamnbanci ba.
“A halin yanzu kune masu warware matsaloli a mastayinku na Janarori dole ku yi aiki tukuru don ci gaban aikin soja,” inji shi.