Jami’ai 2 da sojoji 5 ne aka kashe a ranar Juma’a a lokacin da jami’an Ofureshin Hadin Kai (OPHK) suka fatattaki ‘yan ta’addar Boko Haram (BH) da kungiyar IS da suka kutsa cikin garin Kala Balge na jihar Borno.
Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana haka a ranar Asabar din da ta gabata cewa wasu jami’an rundunar hadin gwiwa ta JTF a arewa maso gabas (NE) uku sun jikkata a harin.
“Abun takaici, jami’ai biyu da sojoji biyar sun biya da mafi girman farashi, yayin da jami’ai uku da suka samu raunukan harbin bindiga ke samun kulawar jami’an lafiya,” in ji kakakin.
Janar Onyema, ya bayyana cewa sojojin sun kashe ‘yan ta’adda da dama da suka zo a kan babura da manyan bindigogi.
A cewarsa, ‘yan ta’addan sun kai hari kan sojojin da aka girke a sansanin ‘Forward Operational Base (FOB) Rann, wani gari mai iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.
“Sojoji sun yi kaca-kaca da ‘yan ta’addan da karfin wuta, lamarin da ya tilasta musu yin watsi da aikinsu tare da janyewa cikin rudani.
“A kazamin yakin da aka yi a Kala Balge, sojoji sun kare garin tare da kashe ‘yan ta’addar BH da ISWAP 26,” in ji kakakin rundunar.
Ya kara da cewa sojojin sun kuma kama motocin yaki na ‘yan ta’adda, da bindigu AK 47 guda 18 da kuma bindigar M-21 guda daya tare da dimbin alburusai. Sojojin sun kuma lalata wasu kayan aiki da dama.
A halin da ake ciki, babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Faruk Yahaya ya jinjinawa jaruman da suka rasu, wadan da suka bayar da farashi mai tsoka wajen kare kasarsu.
Ya kuma yabawa sojoji bisa gallazawar da suke yi a yankin Arewa maso Gabas, musamman irin nasarorin da aka samu a Gajiram da Tumbus.