• Babu gaskiya a batun kai wa Sansanin sojin sama dake Kaduna hari a yau Asabar.
• Tun da safiyar yau ce dai, wasu kafafen yada labaran yanar gizo, su ka ce, an kai hari a sansanin.
• Mai magana da yawun rundunar sojin sama ta kasa ya ce, batun kai harin, bai da tushe balantana makama.
Rundunar sojin sama ta kasa ta karyata rahoton da ke cewa, wasu yan kungiyar tada kayar baya da ake zargin yan Boko Haram ne, sun kai hari a Sannanin ta dake Kaduna a safiyar yau Asabar.
A cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabwet ya fitar yau da rana, ya bayyana rahoton a matsayin “Labaran karya” Wanda ya ce rahoton bai da tushe balantana makama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an soji sun dakile harin yan bindiga
Sanarwar ta ce, “Dukkannin rahoton karyane, domin kuwa Babu wani yunkurin kai hari a Sannanin, a safiyar yau Asabar”. Inji sanarwa.
Kazalika sanarwar tace, Masu yada labaran karya sun sake yin halinsu, inda suka maida hankali kan Sansanin soji sama da ke Kaduna, da suka ce yan bindiga sun kai wa sansanin hari, da sanyin safiyar yau Asabar 26 ga watan Yunin shekarar 2021.
Idan za a iya tunawa dai da sanyin safiyar yau, wasu kafafen yada labarai ta yanar gizo sun ce, Yan ta’addan Boko Haram, sun yi yunkurin kwace ikon Sansanin soji sama dake Kaduna.
Comments 1