Rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole ta yi wa Boko Haram gagarumin illa a maboyarsu dake Alagarno da Dajin Sambisa ta jihar Borno kamar yadda Hedikwatar tsaron Nijeriya ta tabbatar.
Alagarno ta kasance kilomita zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Daraktan watsa labarai na Hedikwatar tsaron, Manjo Janar John Enenche ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a sanarwar da ya fitar, inda ya ce sun dira a wani gini da ke dauke da wadansu manyan shugabannin Boko Haram.
Enenche ya ce ginin yana kilomita 2.3 a arewa maso gabashin Kafa dake karamar hukumar Damboa a jihar, kuma yana cikin duhun ciyawa ne da suke amfani da wurin wajen shirya hare-haren ta’addanci.