Rundunar Sojojin Saman Nigeria (NAF) a ranar Asabar ta ce, an kashe ‘yan ta’adda da dama lokacin da jiragenta 3 suka kai jerin hare -hare a Tsibirin Tumbuns a Tafkin Chadi da Malam Fatori na jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar NAF Air Commodore Edward Gabkwet a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja ya ce, an kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa, kimanin kwale -kwale 20 tare da wadanda ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne da ISWAP suke Shirin hallara wani taro.
Ya ce, rundunar sojojin sama da ke aiki tare da Sojin kasa da kuma Sojin ruwa da sauran hukumomin tsaro, za su ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai sun kawar da dukkan ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a yankin.
Sanarwar ta ce, “Jiragen saman rundunar sojin saman Najeriya (NAF) karkashin Operation Hadin Kai, sun ci gaba da kai farmaki kan‘ yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a tsibiran da yankunan da ke kusa da Tafkin Chadi.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar PDP ta Lashe zaben Karamar Hukumar Zangon Kataf na Kaduna
“Bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 20 ga Oktoba 2021 cewa, kimanin kwale -kwale 20 tare da wadanda ake zargin‘ yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suna taruwa don yin taro a Tsibirin Tumbuns a Tafkin Chadi da Malam Fatori, jirgin NAF guda 3 karkashin Operation Hadin Kai sun yi taho mu gama da Yan Yan bindigan, inda suka kai hare -hare kan masu tada kayar bayan.
“Matukan jiragen sun lura akwai kimanin jiragen ruwa 20 da suka kunshi mutane 5 zuwa 7 da ake zargin Yan ta’adda ne a cikin kowace kwale-kwale, inda suka cakuda bama -bamai da rokoki, sai jiragen saman 3 suka kai jerin hare -hare kan masu tada kayar bayan, yayin da wasu daga ciki suka tsira da ransu.”
“Aikin da rundunar sojan sama ta Operation Hadin Kai ke yi ya sake tabbatar cin galabar yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi”