By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Litinin din data gabata ne rundunar Sojojin Najeriya ta yi nasarar dakile yunkurin wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne na yin garkuwa da wasu ma’aikatan lafiya a jihar Imo.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Birgediya-Janar- Onyema Nwachukwu, Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar Sojojin da aka rabawa manema labarai a Owerri ranar Talata.
A cewar sanarwar, maharan sun yi yunkurin yin garkuwa da gungun likitoci da ma’aikatan jinya da aka fi sani da “Doctors On The Move Africa”.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Likitocin dai suna bada kulawar jinya kyauta ne ga mazauna unguwar Amucha dake karamar hukumar Njaba ta Imo.
“Rundunar sojojin saman Najeriya, 211 Quick Response Group da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa samun bayanan sirri kan shirin aikata laifin, cikin gaggawa suka shiga aikin ceto tawagar likitocin.
“Dakarun sun bi sahun ‘yan ta’addan inda suka tuntubi su a Amauju, a karamar hukumar Isu ta jihar Imo inda aka same su suna aiwatar da dokar zama a gida.
“A fadan daya barke, an kashe daya daga cikin masu laifin, yayin da sauran suka tafi da duga-dugan su, an kuma kai tawagar likitocin zuwa wani wuri mai tsaro.
“Daya daga cikin ‘yan ta’addan da suka tsere da raunukan harbin bindiga, daga baya ‘yan banga na yankin suka kama shi, suka mika shi zuwa ga ‘yan sanda,” in ji Nwachukwu.
Sai dai ya ce sojojin sun kwato bindigar fanfo guda daya, harsashi masu rai guda biyar, Lexus 300 XR SUV guda daya da kuma wayar hannu.