By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 52, Adebayo Akinrinoye, bisa zargin lalata da diyarsa‘ yar shekara 16.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa daya rabawa manema labarai a Ota.
Oyeyemi ya bayyana cewa wanda ake zargin, yana zaune a gida mai lamba 11 Kabiru Close, Idi Opatun tasha, Matogun, Agbado a cikin jihar, an kama shi ne a ranar 23 ga watan Satumba, bayan wani rahoto ta hanyar rubutacciyar takarda da aka kawo hedikwatar ‘yan sanda na Agbado wanda aka azabtar.
Ya kara da cewa, a cikin karar, wanda aka azabtar tayi zargin cewa mahaifinta yana lalata da ita tun tana ‘yar shekara 14. Taci gaba da cewa duk kokarin data yi na hana mahaifin nata aikata wannan abin jahilci ya kasa kunne yaki ji don haka ta kai rahoto ga ofishi ‘yan sanda.
Bayan samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na yanki DPO, ofishin yan sanda na Agbado, CSP Kehinde Kuranga, yayi gaggawar bayyana masu binciken sa zuwa wurin da aka cafke wanda ake zargin cikin gaggawa. ya nemi gafarar ‘yarsa,” inji shi.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘yan sanda, Edward Ajogun, yaba da umurnin a gaggauta mika wanda ake zargin zuwa sashin tallafa wa iyali dake yankin Ota don ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.