Rundunar ‘yan sandan Katsina ta bade kulin da wata mata mai shekaru 42, Mai suna Hajarat Egbunu a shalkwatar ta, kan zargin damfarar Samar da aiki.
Ana zargin Egbunu ta karbi N34,800,000 daga hannun wadanda abin ya rutsa da su, wanda aka ba su takardun kama aiki na karya tare da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS).
Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake zargin tsohowae jami’ar Hukumar kula Shige da Fice ta Nigeria ce wato (NIS), wacce Kuma tayi aiki a Ofishin Hukumar da ke Abuja
A cewar Rundunar yan sandan jihar, wacce ake zargin tayi wa wadanda lamarin ya shafa alkawarin yi sama musu aiki Shelkwatar kungiyar ECOWAS, dake Abuja, wanda kuma zasu rika karbar albashin Naira Milliyan 3 kowanne su, Kuma a duk wata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Sokoto za ta Gina cibiyar Horas da Ma’aikatan Gwamnati
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce, wadanda abin ya shafa daga baya sun gano cewa, wasikun kama aikin da ECOWAS da aka turo musu na karya ne, bayan sun biya Naira Milliyan 3 da dubu dari 5 kowannensu ga wacce ake zargi.
An kama Egbunu a ranar 4 ga watan Oktoba shekarar ran, lokacin da ‘yan sanda suka cafke wani Ibrahim El-Maki wanda ya hada ta, da wadanda abin ya shafa.
Kazalika Rundunar ta zargi wacce ake zargi da damfarar masu neman aiki sama da Naira Milliyan 100 daga wurare daban -daban