By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta gurfanar da wasu mutane tara da suka hada da mata biyu da aka kama da laifin kisan kai da garkuwa da mutane da kuma mallakar bindigogi da sauran laifuka ba bisa ka’ida ba a jihar.
Yayin gabatar da wadanda ake zargin a gaban rundunar ‘yan sanda a jiya a Ado-Ekiti, ‘yan sandan sun ce sun hada da Jimoh Dele, wanda aka fi sani da Dele Petim, wanda aka kama a llorin, jihar Kwara da laifin yin garkuwa da wani fitaccen mai sayar da man fetur a jihar Ekiti a watan Janairun 2021. .
Rundunar ‘yan sandan ta ce Dele ya amsa laifin satar babura, sannan ya yi awon gaba da shaguna da gidaje sama da 10 tare da kwashe sama da babura 12.
Har ila yau, an kama wani Ayo Samuel, mai shekaru 63 da haihuwa, wanda aka kora daga aiki, wanda ya yi ikirarin cewa shi mamba ne na kungiyar masu garkuwa da mutane a jihar. Wani wanda ake zargi shi ne Mubarak Bello, a Igbara-Ode-Ekiti, wanda ya nemi kudin fansa naira 50,000 kan wata mata da aka yi garkuwa da ita Shekina Abdullahi, a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2021.
Wata mata mai suna Nana Sule, wacce ta yi karyar sace ta a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2021, a kan hanyar Ifaki/Oye-Ekiti tare da wasu fasinjoji an kuma kama su tare da gabatar dasu agaban rundunar.
Rundunar ‘yan sandan tace ta kira mijin nata cewa masu garkuwa da mutane suna neman kudin fansa naira 50,000, amma daga baya aka gano cewa ta yi karya ne domin ta samu kudi daga wajen ‘yan uwanta.