Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce wani jariri dan wata 6 ya samu rauni lokacin da ‘yan ta’addar ISWAP suka harba bama-bamai guda biyar a Maiduguri ranar Asabar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdul Umar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa a Maiduguri cewa, ‘yan ta’addan sun harba bama-baman ne daga wajen tsohon filin jirgin sama na Ngomari, bayan jami’ar jihar Borno.
Ya ce bom din sun sauka ne a wurare daban-daban a cikin birnin inda suka yi barna.
Haka kuma ya ce bam na farko ya fado ne a cikin wani gida na wani mutum Ibrahim Abba-Fori, inda ya kona wata mota kirar Honda Civic yayin da daya kuma ya lalata wani daki a gidan Bukar Modu-Kullima tare da raunata jaririyar ‘yar wata mata yar wata 6 da haihuwa Fatima Alhaji-Bukar.
Yace “Wani kuma ya sauka a unguwar Gambari Njimtilo kusa da gidan Ahmed Yahaya, inda ya lalata katangar gidan.
” Bam din na karshe ya fado a gona a kauyen Shuwarin Atom,” in ji shi.
Malam Umar ya bayyana cewa an yi wa yaron dan wata 6 jinyar kananan raunuka a asibitin zamani na Umaru Shehu Ultra sannan aka sallame shi.
Ba a samu asarar rai ba a harin, in ji Kwamishinan, ya kuma kara da cewa an tura karin jami’an ‘yan sanda da sojoji zuwa wajen birnin Maiduguri domin sa ido da kuma sintiri.
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargin zai kawo cikas ga zaman lafiya tare da ba su tabbacin cewa jami’an tsaro a shirye suke wajen kare rayuka da dukiyoyi a jihar.
Comments 1