Rundunar Yan sandan jihar Zamfara ta baje kolin wasu da a ke zargi da hada baki da yan’ bindiga da kuma aikata wasu laifuka.
Daya daga cikin wadanda ake zargin Dan makarantar sakandaren Kwalejin tarayya ta Anka ne, da ake zargin shi da, da kasance wa jagorora a cikin Yan bindigan da suka yi garkuwa da Shugaban makarantar kuma suka bukaci Naira milliyan 3 a matsayin kudin fansa.
Lokacin da ya ke tabbatar da faruwan lamarin, Kwamishinan yan sandan jihar Hussaini Rabiu ya ce, an Kuma kama wani dalibi da ya rubuta wasikar tsoratar wa ga Yar uwan Shugaban makarantar, kan cewa zaryi garkuwa da ita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fashe wani Abu a Kaduna ya jikkata Yara uku
Kwamishinan yan sanda ya kuma ce, Rundunar ta sami wannan nasarar ce, bayan baza jami’an ta, da suka bi,-bi-yi kiiran wayar da aka yi na neman kudin fansa, inda suka kama wanda ake zargi a karamar hukumar Bakura na jihar.
A karshe kwaminan ya ce, wadanda ake zargi sun amsa laifukan su Kuma za’a gurfanar da su a gaban Kotu domin hukun ta su.