Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Sabitu Ibrahim wanda aka fi sani da Aljan a unguwar Kaburma da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Jamie ‘yan sanda na ‘Operation Puff-Adder’ karkashin jagorancin SP Buba Yusuf ta kama Aljan, wanda ke cikin jerin sunayen ‘yan sandan jihar Kano da ake nema ruwa a jallo bisa laifin yin fashi da makami.
Rundunar ‘yan sandan ta ce bayan bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya hada baki da wasu mutane wajen kai wa wani mai Adaidaita Sahu hari a unguwar Dorayi, kuma ya yi amfani da waya wajen kashe shi, amma ya tsere da mugun rauni.
“Bincike na gaskiya ya kai ga kama wani Abdullahi Suleiman, mai shekaru 28, na unguwar Gwale, da Abubakar Muhd, mai shekaru 21, dan unguwar Hausawa.
“Wadan da ake zargin sun amsa cewa sun sayi sassan baburin Adaidaita Sahu da Aljan ya yi fashi daga wani, da kuma wani Adaidaita Sahu da mai rijista da lamba FGE212QX da KAROTA mai lamba 4636 KMC a hannunsu,” in ji kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.
Sai dai Kiyawa ya kara da cewa an kuma samu wasu babura guda biyar daga hannun wani gungun ‘yan fashi da makami kuma wadanda ake zargin sun amsa cewa sun sace su ne a wurare daban-daban.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa sanarwar ta ce“Ayyukan Puff-Adder da aka cigaba da yi a ranar 24/11/2021, an kama Muhd Saidu, mai shekaru 31, dan garin Gobirawa, Yan Yashi, da Abdullahi Tahir, mai shekaru 35, a Kofar Ruwa kwatas.
“An kwato babura biyar (5) da ake zargin an sace su. Wadan da ake gudanar da bincike, wadan da ake zargin sun amsa sace Motocin. Ana cigaba da bincike.”