Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fitar da wani gargadi kan yadda ake amfani da kakakin ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba a shafukan sada zumunta.
Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan sandan suka dakatar da wasu jami’ai biyu na jami’an tsaro saboda karya manufofin kafofin sada zumunta.
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce amfani da kakakin rundunar ya takaita ga jami’an rundunar ne kawai.
KARANTA ANAN: EPL: Liverpool Ta Doke Bournemouth Da Ci 9-0
Wani bangare na sanarwar ya bayya cewa; “Yin amfani da Uniform na ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba, ya takaita ne kawai ga jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya.
“Wannan na zuwa ne biyo bayan dakatarwar da aka yi wa wasu jami’an ‘yan sanda biyu, tare da aiwatar da hakan nan take, bisa karya dokar ‘yan sanda ta shekarar 2020.’’
A wani labarin kuma:
Yajin Aiki: ASUU Ta Musanta Batun Cewa Jami’o’in Jihohi Basu Da Amfani
Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta karyata rahoton da ya ke cewa ta bayyana sunan da ta ayyana jami’o’in mallakin gwamnatocin Jihohi.
a ranar Juma’ar nan ne kafafen yada labarai da dama suka cika da martani dangane da ikirarin da Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi na cewa jami’o’in Jihohi na cikin rudani don haka bai kamata a dauke su da muhimmanci ba.
Ku tuna cewa Farfesa Osodeke a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana a gidan talabijin na Arise TV inda ya yi magana kan wasu batutuwa dangane da ci gaba da yajin aikin jami’oi da ASUU ta fara tun watanni shida da suka gabata.