A kokarin tabbatar da tsaro a jihar, jami’an rundunar hadin gwiwa ta jihar Kaduna guda 312 da aka fi sani da ‘Civilian JTF’ sun kammala samun wani atisayi a kwalejin yan sanda da ke Kaduna.
Shugaban hukumar tsaro na jihar, Shehu Dantudu, a cikin wata sanarwa a Kaduna da ya fitar ranar Lahadi, ya yi bayanin cewa, an horas da jami’an ne domin samun kwarewa kan yadda za su tafiyar da al’amuran tsaro a jihar.
A cewarsa, wasu membobi za su sami irin wannan horo a Kwalejin yan sandan dake Kaduna, a cikin watan Nuwamba shekarar 2021. Duk da bai ambaci adadin jami’an da za su ci gajiyar horon na watan Nuwamban ba, Amma ya ce, hakan na daya daga ciki. kokarin gwamnati na yaki da matsalar tsaro a dukakkanin kananan hukumomi 23 dake jihar.
“Manufar mu ita ce mu taimaka wa gwamnati wajen magance duk wani matsalar tsaro a cikin al’umma, idan muka kama Masu laifi, shine mu mika su ga rundunar yan sanda,” in ji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Katsina ya sanar da Ranar komawar Makaranta a Jihar
Kazalika Sanarwar ta ya Bawa Sufeto Janar na yan sanda, Kwamandan Kwalejin, Shugaban Makarantar, da wadanda ke taimaka wa jami’an hukumar na Civilian JTF ta kowani bangaren.