Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kai samame tare da cafke wasu mutane 30 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da ake kyautata zaton suna da alaka da kashe-kashen ‘yan daba a wasu sassan jihar a ‘yan kwanakin nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mataimakiyar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Jennifer Iwegbu, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa, biyo bayan samun sahihan bayanai na cewa ayyukan kungiyar asiri na ci gaba da gudana a kan titin Oho, Uselu, cikin birnin Benin, a ranar Alhamis din nan, nan da nan jami’an rundunar suka tafi zuwa wurin.
Ta kara da cewa da isar su wajen da lamarin ya faru, jami’an rundunar sun gano gawar wani matashi mai suna Taiwo Edigie mai shekaru 40, inda aka yanke kai aka ajiye a wani wuri daban da inda aka ajiye gawar.
Karanta kuma: Jami’an Yan sanda Sun Kashe Masu Garkuwa 5 A Edo
A cewar sanarwar, an samu makamancin rahoton a wannan rana cewa a kan titin Imuetiyan da ke kan titin Ojo, a Ugbowo, an kashe wani matashi da har yanzu ba a san ko wanene ba dangane da fadan kungiyar asiri da ake yi.
Daga bisani an kai sumame mai tsanani a kewaye inda lamarin ya faru kuma an kama mutane 30 da ake zargi.
An ce ana ci gaba da bayyana bayanan kuma duk wanda aka samu da laifi ko kuma yana da alaka da wani kisan gilla na kungiyar za a gurfanar da shi a gaban kotu idan an kammala shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Abutu Yaro, yayin da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasu, ya tabbatar wa da jama’a irin kokarin da rundunar ta ke yi na ganin babu wata maboya ga masu aikata laifuka.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Kwamishinan ya gargadi mambobin kungiyar Eiye da kungiyoyin Aye Cult kan komawa mummunan hamayyar da suke yi wanda ya yi sanadin mutuwar mambobinsu ko kuma su kasance a shirye don karin kamawa da gurfanar da su a cikin kwanaki masu zuwa.
A wani labarin kuma: ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Shugaban Jam’iyyar APC A jihar Edo
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a ranar Laraba ta ceto Godwin Aigbogun, jigo a jam’iyyar APC daga hannun masu garkuwa.
Aigbogun shi ne shugaban jam’iyyar a gundumar ta 9 dake karamar hukumar Orhionmwon a jihar Edo.