Rundunar Yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane 8, da ake zargin sune keda alhakin kashe wani mutum Mai shekara 30 a karamar hukumar Suletankarkar dake jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da kama mutanan a yau Alhamis a garin Dutse Babban Birnin jihar.
Shiisu ya ce, wadanda ake zargin suna da shekaru ne tsakanin 20 zuwa 40, wadanda kuma sune ake zargi da kitsa farmakan wasu mutane uku dake rayuwa a Rugar Yandamo dake jihar ta Jigawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta dakatar da Buni a Matsayin Shugaban Ruko na Jam’iyar APC
Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun farmaki Rugan ne, bayan sun ga wasu dabbobin su a can da suke zargin an sata ne.
” A ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2021 da musalin karfe 6:30 na yammaci, wasu mutane dake kauyen Amanga na karamar hukumar Suletankarkar suka bibiyi sahun dabbobin su da aka sata zuwa gidan wani Mai suna Alhaji Umaru Sale, dake Rugar Fulani na Yandamo.
“Hakan yasa mutanan suka farmaki Amadu Sale, Babangida Umaru, da kuma Manu Babangida, dukkannin su na Rugar Fulanin Yandamo, da suke zargin sune suka sace musu dabbobin su.” Inji shi.
Jami’in ya kuma ce, dukkannin mutane ukun sun Sami mummunan raunika sanadiyar farmakin, sai dai jami’an yan sanda sun isa murin inda suka kwashe su suka kai su cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na karamar hukumar Suletankarkar, domin duba lafiyar su.
Kazalika Shiisu ya ce, daya daga cikin mutanann Mai suna Sale ya mutu lokacin da Likitoci suke kokarin ceto rayuwar shi.
A karshe ya ce, Kwamishinan Yan sandan jihar Mr Aliyu Sale ya tura rahoton lamrin zuwa sashin binciken manyan laifuka, domin ci gaba da gudanar da bincike.
Comments 1