Wani mazaunin Aboru dake yankin Ipaja a jihar Legas Mai suna Desmond Okoroafor, ya shiga hannun jami’an tsaro, bisa zargin sa da garkuwa da yaron makwabcin shi, mai suna Daniel Chukwudi, Mai shekara 8.
Okoroafor Mai shekara 21 an kama shi ne tare da wani mai suna Egwuonwu Iyke, Wanda ake tunanin da shi ne suka hada baki wurin garkuwa da yaron.
Lokacin da aka kamasu a wani maboyar su dake yankin Ajangbadi, wadanda ake zargin sun bayyana cewa, sun bukaci naira milliyan biyu, da dubu dari biyar wurin iyalan yaron, a matsayin kudin fansa.
KARANTA WANANN LABARIN: Karin Masarautu na nuna inganta Masarautun Gargajiya a Kano, inji Ganduje
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, bayan da Iyayen yaron sun kai rahoto ga rundunar yan sanda a ranar 11 ga watan Yulin Shekarar 2021, sai jami’an binciken sirri, suka fara bi-bi-yan lamarin, Wanda har ya kai ga nasaran kama wadanda ake zargin
Mai Magana da yawun rundunar yansanda jihar Legas CSP Adekunle Ajisebutu a cikin wata sanar wa da fitar a jiya Asabar ya tabbatar da faruwan lamarin, inda kuma ya bayyana cewa, Okoroafor ya yi amfani da amincewar da Iyayen yaron su Kai mai, wurin tafiya da yaron yankin Ajangbadi, kafin a kubutar da shi.
Kazalika Ajisebutu ya ce, Kwamishinan. Yan sanda na jihar Hakeem Odumosu ya bada umarnin gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu.