Rundunar Yan sanda ta kasa tace ta samu korafe-korafe sama da 431 daga ‘yan kasarnan, kan jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya tsakanin watan Yuli zuwa 5 ga Satumba, 2022.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa daga cikin wadancan adadi an warware korafe-korafe 304 tare da yanke hukunci 81 ga jami’an ‘yan sanda da suka yi kuskure.
Wadannan suna kunshe ne a cikin wata takarda da ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ya shirya, yayin da yake bayyana kokarin ma’aikatarsa wajen tabbatar da da’a a tsakanin jami’an ‘yan sanda.
KARANTA ANAN; Gwamna Ganduje Ya Gana Da Kungiyoyin ASUU Na YUMSUK/KUST Wudil
“Kwanan nan, an mai da hankali kan bukatar kwararru da kuma bin wasu dokoki na jami’an ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu na halal.
“Hakan ya sa ake bukatar duba korafe-korafe daban-daban kan matakin ‘yan sanda ta kafafen sada zumunta, da kuma matakin da aka dauka na takunkumin da aka kakaba wa masu karya dokokin da suka tsara yadda jami’an ‘yan sanda ke gudanar da ayyukansu.”
Baya ga takunkumin, Ministan ya kuma ce PPCC a shekarar 2021 ta fara gangamin wayar da kan jama’a da aka yi niyya a shiyyoyin kasarnan guda shida, inda ya kara da cewa an rufe Kudu-maso-Yamma, Kudu-maso-Kudu, Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa-maso-Yamma. An shirya gudanar da shiyyar Arewa maso Gabas a ranar 9 ga watan Satumba a Bauchi.
A wani labarin kuma: Kungiyar Kiristoci Ta Jaddada Ƙin Amincewarta Da Tsarin Yan Takara Musulmai
Shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya CAN a jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata sun sake jaddada kin amincewa da tsarin yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa addini daya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa jam’iyyar APC itace mai wannan tsari na Musulmai zallah a zaben 2023, Sun bayyana cewa ba za su sauya matsayarsu na adawa da tikitin takarar shugaban kasa na musulmi da musulmi ba.