Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, a ranar Litinin, ta musanta rahoton da ke cewa mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga sun kai hari a mahaifar sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce babu kanshin gaskiya a rahoton da ke cewa al’ummar kauyukan Dabna da Kwabre da ke gundumar Dagwaba ta karamar hukumar Hong sun Tsere sun bar gidajensu sakamakon harin da ake zargin an kai musu.
Nguroje ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa, rundunar ‘yan sandan ta baza jami’an yaki da ta’addanci da masu garkuwa da mutane, da kuma jami’an sirri a yankin.
Ya ce kawo yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaro cewa an kai hari a yankin.
“Rundunar ta samu bayanan da ba a tantance ba cewa mutane na gudun hijira daga wasu kauyuka sakamakon hare-haren da ake zargin Boko Haram da kai wa.
“A matsayinmu na jami’an tsaro, ba ma wasa da duk wani bayani da ya shafi rashin tsaro.
Nguroje ya shaida wa NAN cewa, “Nan take rundunar ta tura jami’an yaki da ta’addanci da kuma jami’an leken asiri zuwa wuraren da ake zargi, kuma kawo yanzu babu wani rahoton kai hari ko mutanen da suka tsere daga kauyukan su.” Inji Nguroje.