Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun kai hari kan babban mataimaki na musamman kan harkokin addinin Kirista ga gwamnan jihar Bauchi, Zakka Luka Magaji.
Da yake tabbatar da harin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan, SP Ahmed Wakili, ya ce ‘yan bindigar da yawansu ya kai bakwai sun kai farmaki gidan mamacin da ke Birshin, wani yanki na al’ummar jihar.
Ya kara da cewa rundunar ta samu kiran waya da misalin karfe 12:13 na yammacin ranar Juma’a cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan hadimin gwamnan.
Wakili ya ci gaba da cewa, “A lokacin da rundunarsu ta samu wannan kiran na gaggawa, kwamishinan yan sandan jihar, ya umurci sashen E-DPO da ya dauki matakin gaggawa.
KARANTA ANAN: Lalacewar Hanyoyi Ta Sanya Wasu Gwamnoni Kokarin Samar Da Jirgin Sama
Kuma guda cikin Baturen yan sandan jihar, ya jagoranci tawagarsa tare da wasu kwamandojinsu domin gaggawar shiga tsakani wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa cikin daji.
“Wani mutum mai shekaru 32 da haihuwa mamba na Cocin Christian Life da ke zaune tare da Zakka ya ji rauni yayin afkuwar lamarin.”
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da cewa jami’an da ke wurin domin ceto wadanda lamarin ya shafa sun garzaya da wanda abin ya shafa asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa domin kula da lafiyarsa.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa za a kara zage damtse wajen zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da jan hankalin mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu domin mutanen su na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin alumma.
Da yake mayar da martani, mai taimaka wa, Zakka Magaji, ya ce shi ne babban wanda aka kai harin duk da cewa har yanzu ba a san musabbabin harin ba.
A wani labarin kuma: ‘Najeriya A Kalubalan Ambaliyar Ruwa,’ FG Ta Roki Jihohi Da Su Dauķi Mataki
Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta roki hukumomi a jihohi daban-daban da su jajirce wajen ganin an kiyaue kara samun ambaliyar ruwa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Babban Daraktan hukumar NIHSA, Clement Nze, wanda ya bayar da sanarwar a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan a Abuja, ya bukaci jihohi da su dauki matakan da suka dace don hana mummunar matsalar ambaliyar ruwa a shekaru masu zuwa.