Rundunar Yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da garkuwa da Cif Idoko Emmanuel, Paul Onoja da Blessing Akoh a yankin Emonoja na jihar.
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar ASP William A. Aya ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.
Ya ce jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin Olamaboro, karkashin jagorancin Jami’in‘ Dan Sandan dake kula da yankin, tare da taimakon ‘yan banga na yankin, sun bi sahun masu garkuwa da mutanen zuwa cikin daji.
Aya ya Kara da cewa, da misalin karfe 6 na yammacin ranar Asabar, ‘yan bindigar sun yi watsi da wadanda suka yi garkuwa da su, sannan suka tsere lokacin da jami’an da ke aikin ceto ke kusa da su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Yan sanda sun ceto Malamin Jami’ar Kogi daga Hannun Yan bindiga
Kazalika ya ce, mace daya tilo ce, ta jikkata a halin yanzu, Kuma tana karbar kulawar likitoci a wani asibiti dake jihar.
A karshe ya Kuma ce, har yanzu ana ci gaba da kokarin kamo masu garkuwa da mutanen.
A wani labarin Kuma na daban.
An samu barkewar cutar a kusa da yankin Ireti Ayo na Ilesa, yayin da aka gano wasu ma’aurata, Eso Olasunkanmi da Eso Fisayo sun mutu bayan sun ci a cikin abincin mai dauke da cutar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin data gabata, an gano ma’auratan ba su da rai a cikin dakin su.
Duk da haka an tattara cewa ma’auratan sun ci abincin daren Juma’a amma yanayin mutuwar su mai ban mamaki bai bayyana ba tukuna.
Wani mazaunin yankin, Wale Banjo, yace babu wanda ya san abin daya same su amma an gan su da farko a ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba saboda hutun da ake yi sai kawai ganin gawarwakinsu a kayi da yamma.
Opalola ya bayyana cewa an kai gawawwakin zuwa asibiti domin gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwarsu.
“An kai gawar ma’auratan asibiti domin a binciki gawar. Sakamakon zai iya taimaka mana mu gano sirrin dake bayan mutuwarsu.ya kara da cewa “A halin yanzu, ba zan iya bayyana abin da ya kashe su ba har sai bayan kammala binciken gawar.”
Comments 1