Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar malamin Kwalejin fasaha na jihar, Malam Bzegu, wanda wasu ‘yan bindiga suka kashe da sanyin safiyar ranar Alhamis din da ta gabata a gidansa da ke Bajabure da ke wajen birnin Yola.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sulieman Nguroje ne ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana marigayin a matsayin malami a sashen injiniya na kwalejin fasaha ta Yola a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/yanzu-yanzu-an-kara-farashin-man-fetur-a-najeriya/
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Nguroje ya ce: “Kwamishanan ‘yan sandan jihar, Sikiru Akande, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a safiyar yau inda ya bayar da umarnin a gudanar da bincike cikin gaggawa da nufin cafke wadanda suka aikata laifin.
“Kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi na karuwa a jihar tare da haddasa rashin barci ga yawancin mazauna jihar.”
A halin da ake ciki kuma, wani ganau ya ce maharan sun kutsa cikin gidan malamin inda suka yi ta harbe-harbe da dama a cikin kirjinsa har sai da ya ce gagarinku nan, yayin da matarsa ta nuna ba dadi.
A cewar ganau, “’yan bindigar sun kai farmaki gidan marigayin ne da misalin karfe 3 na dare. A ranar Alhamis din da ta gabata kuma suka shiga gidansa,” ya kara da cewa kawai sun kashe malamin ne amma ba su kwashe kayansa ba.
Ya kara da cewa: “Sun zo ne da misalin karfe 3 na safe yunkurinsu na hudu ko na biyar ne, kuma ba mu san dalilin da ya sa suka kashe shi ba.