By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da sace wasu matafiya a kalla bakwai da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi a hanyar Geregu zuwa titin Ajaokuta a jihar.
Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da lauya, likita, da wasu biyar da ke tafiya a cikin motoci daban-daban da misalin karfe 2 na rana a ranar Talatar da ta gabata lokacin da masu garkuwa suka kai musu hari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Yobe Ta Rufe Ofishin Dillalan Filaye Kan Rashin Samun Izinin Lasisin Aiki
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun killace kan titin na tsawon sa’o’i da dama, inda suka rika harbe-harbe akai-akai, kuma ana cikin haka an yi awon gaba da fasinjoji da dama yayin da wasu da dama suka samu raunukan harbin bindiga.
Majiyar mu ta kuma bayyana sunayen wadanda aka sace sun hada da Mista Joe Abba, da matarsa, da kuma Barista Abba Aduojo wadanda suke dawowa daga wani biki a wani kauye da ke kusa da Aloma a karamar hukumar Ofu ta jihar.
Har ila yau, an sace wani likitan da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, wanda aka ce yana kan hanyarsa ta komawa Lokoja daga wani aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Anyigba.
“An harbi matar abokina a kafarta kuma a halin yanzu tana samun sauki a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Lokoja,” in ji wani dan uwan wadanda abin ya shafa.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, William Aya, rundunar ta samu labarin hare-haren da ‘yan bindigar suka kai tare da tsara mutanen da ke aiki a yankin domin ceto su.
“An sace mutane bakwai, an ceto mutane shida da raunukan harbin bindiga, an kuma kwato motoci shida a wurin da lamarin ya faru,” inji shi.
Ya kara da cewa ‘yan sanda da suka hada da ‘yan uwa jami’an tsaro da ’yan banga sun hada kai don tseratar da wuraren domin kubutar da mutane bakwai da aka sace.
Comments 1