Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Mista Lawal Abubakar, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin tashin gobara a ofishin INEC da ke karamar hukumar Igboeze ta Arewa.
Idan dai za a iya tunawa,. Dimokuraɗiyya ta rawaito muku yadda gobarar ta tashi da misalin karfe 11 na dare a ranar 3 ga watan Yuli a ofishin INEC na karamar hukumar Igboeze ta Arewa da ke Ogurute a yankin Enugu-Ezike na karamar hukumar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), DSP Daniel Ndukwe, ya fitar a Enugu ranar Litinin.
Ya ce watakila gobarar ta tashi ne daga bayan ginin.
Ya kara da cewa, jami’an ‘yan sanda da suka tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru bayan samun labarin, tare da taimakon jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Enugu ne suka kashe gobarar, ta yadda aka dakile barnar da aka samu a unguwar.
“Saboda haka, CP ya ba da tabbacin cewa umurnin zai yi duk mai yiwuwa don gano musabbabin faruwar lamarin tare da daukar matakin da ya dace.
Kwamishinan ya kuma bukaci mazauna yankin da su baiwa ‘yan sanda sahihin bayanai da kuma bayanan sirri kan binciken da ake yi.
Hukumar ta ce an killace yankin domin kiyayewa da kuma gudanar da bincike.
A halin da ake ciki, INEC ta ce wasu ‘yan bindiga a ranar Lahadi sun kona ofishinta da ke karamar hukumar Igboeze ta Arewa tare da lalata akwatin zabe kusan 748.
Mista Festus Okoye, kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na kasa INEC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta ce: “Kwamishanan zabe na jihar Enugu, Dokta Emeka Ononamadu, ya ruwaito cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishinmu na karamar hukumar Igboeze ta Arewa.