By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja FCT sun kama wanda suke zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ‘yan fashi da makami mutum uku.baya da haka a yayin gudanar da aikin nasu sun kama karin wasu mutane 23 da suke zargi da aikata laifuka daban daban ciki harda satar mota, zamba da kuma tsafi.
Kafin gabatar da masu laifin ga ‘yan jaridu a yau Juma’a a hed kwatar ‘yan Sandan dake Abuja kwamishinan ‘yan Sanda CP Babaji Sunday yace “rundunar ‘yan Sanda ta birnin tarayya Abuja FCT ta samu muhimman a bubuwa irin su ma’adani dutse wanda suke rike dasu babusa ka’ida ba, da kuma samun masu garkuwa da bindiga kirar Ak 47 guda biyu da alburusau guda 60.
A yayin gudanar da aikin ‘yan sandan Dawaki sun kama Danjuma Mohammed mai shekaru 38 dauke da Ak 47 guda biyu da kuma harsasai guda 60 a yayin da yake tafiya maboyar sa dasu.
Kazalika a cikin binciken nasu sun kama Yahaya Musa mai shekaru 47 wanda yana daya daga cikin masu garkuwa da mutane inda sukaje karbar kudin fansa a Bwari Kwali axis dake FCT.
Sauran wadanda ake zargi sun hadar da Adamu Jibrin mai shekaru 37 da Mohammed Dahiru Husseini mai shekaru 38 da kuma Abubakar Ya’u mai shekaru 35 inda suka hadu dan aikata laifuka kuma aka samu nasarar kama su a Karshi axis.
Bincike ya nuna cewa sunyi barazanar yin garkuwa da dan uwan Adamu Jibrin tare da karbar kudin fansa har naira 750,000 bayan kuma basuyi garkuwa da shiba, rundunar ‘yan Sanda tace zata mikasu kotu dan su girbi a binda suka shuka da zarar sun kammala bincike.