Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a ranar Litinin ta tabbatar da kashe mutane uku a wani hari da aka kai kauyen Tse Ngban da ke unguwar Nyiev a karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Daily Post ta ruwaito cewa, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an aika gawar wadanda suka mutun zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
KARANTA WANNAN LAABRIN: Femi Falana Ya Baiwa Rundunar Yan Sandan Najeriya Awanni 24 Kan….
Tun da farko, wani mazaunin yankin, Mista Julious Moab, ya ce lamarin ya faru ne a daren Lahadi.
A cewarsa, mutanen kauyen sun gudu zuwa wani wuri mai aminci tun bayan da suka lura an kashe mutane ukun.
A cewarsa, maharan sun yiwa Tse Ngban kawanya ne da misalin karfe 7 na dare inda suka yi ta’addanci kan mazauna garin, inda ya kara da cewa wata mata ta mutu a nan take yayin da sauran biyun suka mutu jim kadan bayan harin sakamakon raunukan da maharan suka yi musu.
A WANI LABARIN KUMA: Da Dumi-Dumi: Yan Majalissar Imo Sun Tsige Kakakin Majalissar Jihar
Majalisar dokokin jihar Imo, da yammacin ranar Litinin, ta tsige kakakinta, Kennedy Ibe.
Majalisar ta kuma zabi Emeka Nduka a matsayin sabon kakakinta.