By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tace ta kwato dabbobin gida guda 170 na wasu shugabannin ‘yan bindiga da suka mutu a wani samame da suka kai maboyarsu a kauyen Dage dake karamar hukumar Dutsin-ma a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka a ranar Asabar, yace ba wanda aka kama a cikin su.
Isah ya bayyana sunayen ‘yan bindigar da suka mutu a matsayin Kabiru Master da Tashi Alhaji Musa, wadanda aka kashe a jihar a rikicin shugabanci makonni biyu da suka gabata.
Yace, “A ranar 2 ga watan Disamba, 2021, da misalin karfe 8 na safe ne aka samu bayanai masu inganci cewa kimanin makonni biyu da suka gabata, wasu gungun ‘yan bindiga guda biyu karkashin jagorancin Kabiru Master da wani Tashi Alhaji Musa, sun samu rashin fahimtar juna wanda ya haifar da mummunan Fada a dajin Sabon Birni dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda ya yi sanadin kashe Tashi Alhaji Musa da wasu ‘yan bindiga tara.
“Dukkan shugabannin biyu ‘yan asalin kauyen Dage ne, karamar hukumar Dutsin-ma ta jihar Katsina.
Sai dai Bayan haka, wani rahoton leken asiri da hukumar ta fitar ya nuna cewa wasu ‘yan bindiga da suka tsira daga fadan sun dawo da wasu dabbobin gida da ake zargin satar su a kayi. Sakamakon haka rundunar ta kai farmaki tare da kai samame gidajensu a kauyen Dage, karamar hukumar Dutsin-ma.A ci gaba da binciken an gano shanu 67, tumaki 60, awaki 40 da jakuna uku.”
Ya kara da cewa ‘yan sandan sun kuma kwato bindiga kirar AK47 guda daya a wani samame da suka kai a karamar hukumar Bakori a jihar.
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar 1 ga watan Disamba, 2021, da misalin karfe 5:20 na yamma, an samu labarin cewa wasu ‘yan kungiyar Yansakai da ba a san ko su wanene ba, daga kauyukan Kandarawa/Garanguzai na karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, sannan sun kara kai hari a kauyen Gidan Gamji Fulani, dake karamar hukumar Kankara, inda suka yi harbi ba kakkautawa. da makamai masu haɗari.Yansakai sun kashe mutane biyu tare da kona sansanin kafin isowar tawagar ‘yan sanda dake sintiri a yankin.”