By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja tace ta ceto wasu mutane takwas da aka yi garkuwa dasu a dajin Sarkin Pawa dake karamar hukumar Munya a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Wasiu Abiodun, shine wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis a Minna, inda yace an yi garkuwa da wadanda aka ceto ranar Lahadi a karamar hukumar dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Abiodun yace bisa samun sahihin bayanan sirri da jami’an ‘yan sanda sukayi dake sintiri a kan titin Lukuma/Shafe na Sarkin Pawa sun ceto wadanda lamarin ya shafa a ranar Laraba da misalin karfe 5 na yamma.
Abiodun ya kara da cewa bakwai daga cikin wadanda aka ceto sun fito ne daga karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina yayin da takwas da aka ceto kuma ‘yan asalin karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna ne.
Yace binciken farko ya nuna cewa wadanda lamarin ya rutsa dasu sun fara tafiya ne daga garin Kankia dake jihar Katsina a ranar 21 ga watan Nuwamba inda suka nufi Abuja lokacin da aka yi garkuwa dasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
“A yayin da ake zayyana wadanda abin ya shafa, an gano cewa an kai su dajin Kofa dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna,” inji shi.
Abiodun ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin kamo ‘yan bindigar da suka gudu, sannan yace “Muna kira ga mazauna karkara dasu taimaka a ci gaba da yaki da masu aikata laifuka da bayar da bayanan sirri da zasu taimaka wa ‘yan sanda wajen cafke barayin,” a cewar sa.