Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Mista Ayuba N. Elkanah ya mika kudi naira miliyan biyu da dubu dari biyar ga iyalan ‘yan sanda biyar da suka mutu a bakin aiki.
A cewa wata sanarwar manema labarai da aka sanyawa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar ta hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu, ya gabatar da cakin kudin din na ci gaba da shirin inshorar jin dadi da IGP yayi ga iyalan jami’an ‘yan sanda da suka mutu.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/jihohi-18-na-tarayyar-najeriya-suna-da-rauni-kan-tsarin-kiwon-lafiya-rahoto/
CP ya samu wakilcin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda,na ma’aikatar kudi da mulki, DCP Olubenga Adepoju.
“Kwamishanan ‘yan sandan ya yabawa Sufeto Janar na ‘yan sandan bisa yadda ya damu da jin dadin jami’an ‘yan sanda.
“CP ya bayyana matakin a matsayin wanda ya dace kuma zai ci gaba da tafiya tare da rage radadin da iyalan jami’an ‘yan sandan da suka mutu ke fuskanta tare da kara tabbatar wa da Sufeto Janar na ‘yan sandan cewa jami’an rundunar za su ci gaba da yin bakin kokarinsu wajen sauke nauyin da aka dora musu. wajibi ne don dorewar zaman lafiya, tsaron jihar Zamfara,” inji shi.
A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci wadanda suka ci gajiyar kudin da su yi amfani da kudin bisa ga gaskiya, inda ya ce, “a cikin watanni 10 da suka gabata rundunar ta samu irin wannan cakin kudin daga babban sufeton ‘yan sandan kasar har sau goma, kuma ta gabatar da makamancin haka ga wadanda suka amfana.
Daya daga cikin iyalan da suka ci gajiyar Favour Peter, wacce ta yi magana a madadin sauran wadanda suka amfana, ta godewa babban sufeton ‘yan sanda bisa wannan karimcin tare da alkawarin yin amfani da kudin ta hanyar da ta dace.