By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Lahadi, ta sanar da cewa ta samu nasarar cafke wasu mutane 21 da ake zargin shahararun ‘yan fashi da makami ne da kuma abokan hadin gwiwa 48 yayin gudanar da samamen da ta kai a cikin watan Satumba.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda SP Muhammed Shehu, a jihar shine wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Gusau, kan nasarorin hukumomin tsaro a jihar.A cewar sa an kuma kashe ‘yan bindiga biyar a jerin sunayen da jami’an tsaron suke nema.
“Tun bayan aiwatar da sabbin matakan tsaro na Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, wata guda daya gabata ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kai hare hare kan wuraren da aka gano maboyar ‘yan bindiga ne dan kawar da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka daga cikin jihar.sannan an daina biyan diyya ga ‘yan ta’adda ta hanyar dangantakar wadanda aka yi garkuwa dasu saboda yadda ake aiwatar da matakan tsaro, ta yadda sadarwa tsakanin ‘yan fashin da masu yi musu bayani ya zama mai wuya, “in ji Shehu.
Kazalika ya kara da cewa, a sakamakon haka, wadanda aka sace sun zama abin dogaro ga ‘yan bindigar kuma an sake su ba tare da wani sharadi ba, bayan da aka gudanar da bincike da inda ‘yan sanda suka ceto su.
Shehu yace, ‘yan sanda ta hanyar aikin da suke ci gaba da yi, sun yi nasarar cafke shahararrun’ yan bindiga 21 a wurare daban daban na jihar, inda aka kashe biyar daga cikin ‘yan bindigar yayin farmakin, a wurare daban daban, an yi musu bayani kuma sun sake saduwa da danginsu.
A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don tabbatar da matakin da kowanne daga cikin wadanda ake zargin ya shiga hannu daga nan za a gurfanar da su a gaban kuliya daban daban, sannan Shehu ya yi kira ga mazauna yankin da su yi hakuri tare da baiwa hukumomin tsaro goyon bayan da ake bukata don kawar da duk masu laifi a jihar, dan dawowar doka da oda.