Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kano ta bayyana labarin harbin bindiga da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi a ofishinsu a matsayin maras tushe, rashin gaskiya da kuma karya
Kakakin shiyya ta daya a rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abubakar Ambursa, ya ce “a cewar wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai wa yankin mu hari ba komai ba ne illa karairayi da wasu batagarin mutane suka kulla.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Ficewar Sa Daga APC, Sanata Magnus Abe Ya Sanar Da Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar SDP
“Na kasance a ofishin tun karfe 9 na safiyar yau kuma babu wani rahoto daga kofofin yankin cewa wasu mutane sun yi harbin bindiga.”
“Kar ku manta akwai masallacin Juma’a a shiyyar kuma kamar yadda a lokacin suka ce wasu ‘yan ta’adda sun yi harbin lokacin Sallah ya yi saboda mun yi sallarmu da karfe 1:00 na rana, don haka ba zan iya gane inda labarin ya fito ba.”
“Lokacin da kuka yi min magana game da yiwuwar faruwar lamarin, sai na je bakin kofar hedikwatar na yi tambaya kuma ba a samu rahoton haka ba, sai tawagar ‘yan sandan mu ta binciki wadanda ke wajen da ke halartar Sallar Juma’a.
“Sun tsaya a bakin kofar; babu wanda ya ce ya ji karar harbin bindiga”.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun yi harbin kan mai uwa da wabi a hedikwatar ‘yan sanda ta Zone 1 da ke kan titin BUK a Kano.
A cewar majiyoyin tsaro, ‘yan ta’addan sun zo ne a cikin motoci uku da misalin karfe 12:30 na ranar Juma’a inda suka yi harbi da yawa a ginin sannan suka zurfafa.
Majiyar ta ce ana kara karfafa tsaro a kewayen hedikwatar domin dakile yiwuwar Karin kai hare-hare daga ‘yan ta’addar.