Daga Sabiu Musa Kano
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kakakin ‘yan sandan jahar kano Abdullahi kyawa yayin hira da manema labarai inda yace dole mutane da masu unguwanni su kula da waye za a ba hayar gida.
Hakan ya biyo bayan kamun da akayiwa wadanda suka yi garkuwa da magajin garin daura a satin da ya gabata a yankin jemagu dake karamar hukumar kumbotso ta kano inda yanzu haka ake ci gaba da bincike kan lamarin inda ake zargin Wani limamin yankin tunda yana da hannu wajen bada hayar gidan ga masu garkuwa da mutane.
Abdullahi ya kara kira da mutane su hankalta yadda zasu rika gane bakuwar fuska inda yace ta haka ne za a samu zaman lafaiya da kuma tona asirin duk wani bata gari inda har ya bada lambar ko ta kwana Sannan yace kar a ringa kira na dakile Wanda aka fi sani da miss call a turance.
Yace baza su saurarawa duk wanda aka samu da irin Wannan abun kaicon da Allah wadai ba inji Abdullahi.