By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tace ta dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Gidan Duka, dake karamar hukumar Kankara, a jihar, inda ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa dasu a garin Safana.
Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Gambo Isah, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa daya raba wa manema labarai, ranar Lahadi, a Katsina, yace an kuma kwato shanu 38 da tumaki 11.
“A yau, 14 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 ‘yan fashi da makami dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai hari kauyen Gidan Duka, karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da wasu dabbobin gida da ba a tantance adadinsu ba.
“DPO Kankara da tawagarsa sun yi gaggawar amsa kiran da aka yi musu, suka bi sawun ‘yan bindigar.
“Rundunar ta hadu da ‘yan bindigar a kauyen Danmarabu inda suka yi musu luguden wuta. wanda a sana diyyar hakane ‘Yan fashin suka tsere zuwa cikin dajin, inda suka saki duk wasu dabobin da aka sace.sannan “Rundunar ta kuma gano wani babur wanda ‘yan fashin suke aiki dashi; yayin da ake ci gaba da Gudanar da bincike.”a cewa Isah.
kazalika, yace bisa sahihin bayanan sirri, da rundunar ta samu tayi nasarar ceto mutane 11 da aka yi garkuwa dasu daga Sabon Garin Safana, inda ya bayyana cewa, “an kubutar da wadanda harin ya rutsa dasu ne daga maboyar ‘yan bindiga, dake wajen kauyen Tsaskiya, a karamar hukumar Safana ta jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa idan za’a iya tunawa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Sabon Garin Safana a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2021 tare da yin garkuwa da 11 daga cikin mutanen kauyen.