Gabanin zaben 2023, jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Nasarawa sun gargadi jam’iyyun siyasa daban-daban da magoya bayansu da su guji duk wani tashin hankali na zabe yayin da suke gudanar da yakin neman zabe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Adesina Soyemi ne ya yi wannan gargadin a wani taro da shugabannin jam’iyyu na jihar da sakatarorin jam’iyyun siyasa daban-daban na kananan hukumomi 13 na jihar da kuma kwamishinan zabe REC na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, a Lafiya a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwankwaso Ya Yi Watsi Da Gayyatar Taron Tattaunawa Da ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa taron ya zama wajibi ne biyo bayan umarnin da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mista Alkali Baba ya bayar na ganin an gudanar da zaben 2023 cikin nasara.
Tun da farko, Kwamishinan Zabe na Jihar Nasarawa, Uthman Ajidagba, ya bayyana aniyar INEC na gudanar da sahihin zabe a 2023.
Ajidagba, wanda ya samu wakilcin sakataren hukumar ta INEC na jihar, Mista Usman Wase, ya ce hukumar za ta samar da daidaito ga dukkanin jam’iyyun siyasa, inda ya yi kira da a ba su hadin kai wajen ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihar.
A tasu gudunmuwar daban-daban, Shugaban Jam’iyyar Labour ta Jihar, Mista Alexander Emmanuel; Sakataren Gamayyar Jam’iyyar APC na Jiha, Mista Hassan Abubakar; Sakataren jam’iyyar PDP na Jiha, Mista Adamu Bako, da sauran su sun yaba wa ‘yan sanda bisa wannan shiri tare da jaddada aniyarsu ta bin dokokin da za su jagoranci zaben 2023.
A wani labarin kuma, 2023: ‘Akwai Hadari A Mika Kasa Ga Shugaban Mara Lafiya’ – Mataimakin Atiku
Gabanin babban zaben 2023, mataimaki na musamman kan hulda da jama’a ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Phrank Shaibu, ya yi gargadin cewa yana da hadari a mika kasa ga shugaban da ba shi da lafiya.
Ya ce a halin yanzu Najeriya na cikin wani mawuyacin hali inda kowane bangare na tattalin arzikin kasar ke cikin rugujewa, don haka bai kamata a mika kasar ga shugaban kasa mara lafiya ba.