Rundunar Yan Sandan Nigeria ta amince da Sabon tsarin shiga ga jami’anta Mata, Wanda ya Hadar da amfani da Hijabi ga Mata musulmi.
Wata sanarwa da Jaridar Intel Region ta yo tozali da ita, ta bayyana cewa Hijabin da aka amince suyi amfani da shi irin karamin nan ne, Sai Dan kunne da kuma Jakar Hannu, da takalmi Mai ado da suke ra’ayi.
To Sai dai sanarwar ta ce wadancan tsarin shiga shima ra’ayi me, ko da kuwa Jami’ar ta kasance musulma, wato dai ba wajibi bane amfani da su.
Kazalika Rundunar ya kuma Bukaci Jama’an da su ci gaba da bin Dokokin da Hukumar ta shardanta musu, Sau da kafa.
Duk kokarin ji daga bakin Kakakin Rundunar na Kasa, dangane da wannan Batu abun ya ci tura, domin kuwa ya bayar da uzurin Yana aiki, Kuma har kawo lokacin wallafa wannan rahoto Bai tuntube mu ba.