• Rundunar yan sandan jihar Ondo ce ta baje kolin wadan da ake zargin da fashi da makami da kuma fyade.
• Mutun Sha biyu ne rundunar ta ke zargi da aikata fashi, 3 kuma da zargin laifin fyade.
• Kwamishinan yan sandan jihar Ondo ne ya baje kolin wadan da ake zargin a shalkwatar rundunar jihar
Rundunar yan sandan jihar Ondo ta baje kolin wasu mutun goma sha biyar, da take zargin na da hannu wurin yin fashi da makami da kuma fyade.
Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Bolaji Salami ne ya baje kolin wadanda ake zargin, a shelkwatar rundunar yan sandan jihar da ke Akure babban birnin jihar .
“Daga cikin wadanda ake zargin, an kama 12 ne da zargin fashi da makami, inda aka kama 3 da zargin fyade, Wanda da suka aikata laifin lokacin suna cikin maye” injishi
Salami ya ce, dukkannin wadanda ake zargin sun amsa laifin na su, Wanda su ka aikata, cikin watan Mayun da ya gabata, da kuma watan Yunin da muke ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nan da mako 3 Bala Muhammed zai bayyana matsayar sa akan takaran Shugaban kasa
Ya kuma Kara da cewa, an kama Seyi Adeyemi da Emmanuel Sunday ne, da zangin fashi da kuma kisan wani Mai suna John Ede da suka kwace mai mashin kiran Bajaj.
Lokacin da ya ke karin haske dangane da lamarin ya ce, an kama wadanda ake zargin dauke da makamai.
A karshe ya kuma yi kira ga mazauna jihar, dasu cigaba da bai wa rundunar yan sanda bayanan da suka da ce, domin magance matsalar tsaro a fadin jihar baki daya.
Comments 1