Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu manyan jigagajin masu Garkuwa da mutane, da suka addabi mutanen da basuji ba, ba su gani ba a fadin jihar.
Bayanin hakan nakunshe ne a cikin wata sanar war da ta sami sa hannun Mai magana da yawun rundar na jihar DSP Sulieman Nguroje, Wanda ya bayyana cewa, an kama dukkanin wadanda ake zargin ne a maboyan su daban-daban, bayan samu wasu ingantattun bayanan sirri akan su.
A cewar jami’in, binciken da aka dukufa akan wadanda ake zargin, an kwato wayoyin hannu guda 18, da kuma Layin waya na kamfanoni sadarwa daban-daban guda 23.
Sanar war ta kara da cewa, “Wadanda ake zargin, sun amsa laifin su lokacin da ke yi musu tambayoyi, kan garkuwa da wani Mutum Mai suna Alhaji Sale Idi dake garin Farang na karamar hukumar Fufore, da kuma wani Mai suna Ya’u Adamu na kauye Ganye , da Jones Hayatu dake kauyen Kojoji a karamar hukumar Jada na jihar, bayan su amshi makudan kudade a matsayin kudin fansa” inji sanarwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nasarawa United za ta tafi hutun mako biyu
Hakan ne ya sa Kwamishinan Yan sandan jihar, ya umarci jami’an SIB da su yi duk mai yiwuwa, wajan tabbatar da sun kama wadanda ake zargi.
A cewar sanar war, Kwamishinan Yan sandan jihar ya kuma ja hankalin al’umar baki daya, da su ci gaba da bai wa jami’an yan sanda ingantattun bayanai, kan mutanen da basu yadda da su ba a unguwan in su. Domin dakile ta’addanci.
A karshe kwamishinan yan sandan jihar ya ba da umurnin a gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin, sannan ya tabbatar wa da al’umar jihar cewa, za’a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.
Comments 1