Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tsare wani dan jarida Malam Umaru Maradun, wakilin Jaridar Leadership, bisa wani dalili da ba a bayyana ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba Elkanah, ya tabbatar da tsare dan jaridar, ga Ibrahim Maizare, shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya reshen Zamfara, wanda ya zanta da shi ta wayar tarho.
CP Elkana yace zai yi duba na tsanaki, kan batun dan jaridar, kafin daga bisani yayi karin haske kan abinda ke faruwa.
An kama Maradun ne a mahaifarsa dake karamar hukumar Maradun, wanda unguwar tasu ta kasance mahaifar Gwamna Bello Matawalle na Zamfara.
An kama shi ne da sanyin safiyar ranar Asabar kuma aka kai shi sashin binciken manyan laifuka na rundunar (CID) da ke Gusau, babban birnin jihar.
Maizare ya jagoranci jami’an NUJ da na ‘yan jarida zuwa hedikwatar ‘yan sanda domin a sako shi amma hakan bai samu ba.
Yanzu haka dai Maradun yana tsare a sashin binciken manyan laifuka (CID) inda shugabannin NUJ suka nemi belin sa amma ‘yan sanda suka ki amincewa.